(ABNA24.com) Shamkhani ya bayyana haka ne a taron binciken inda aka kwana dangane tattara bayanai na shari’ar kisan Shahid Sulaimai a yau Asabar a nan birnin Tehran.
Shamkhani ya kara da cewa Amurka da HKI ba su tsani shahidai biyu, wato Sulaimani da kuma Abu Mahdi Almuhandis ba, sai don irin rawan da suka taka wajen warware makirce-makircen da Amurka da Isra’ila suka kullawa mutanen yankin ba.
Kafin haka dai babban mai gabatar da kara na birnin Tehran, Ali Al-Kasi Mehr ya bayyana a ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata, kan cewa mutane 36 ne bincike ya tabbatar da cewa suna da hannun kai tsaye wajen kissan Shahid Sulaimani.
Sannan ya kara da cewa, daga cikinsu har da shugaban kasar Amurka mai ci Donal Trump da kuma wasu jami’an sojojin Amurka. Mehr ya kara da cewa gwamnatin kasar Iran ta bukaci taimakon ‘yansandan kasa da kasa Intapol don gurfanar da wadanda mutane a gaban kuliya.
342/